An kashe mutane da dama a garin Potiskum

An kashe mutane da dama a garin Potiskum Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Jama'ar yankin sun zargi jami'an tsaro da kasa basu tsaro

An kashe mutane da dama a wani hari da aka kai a babbar kasuwar shanu a garin Potiskum na Arewacin Najeriya, kamar yadda shaidu suka shaida wa BBC.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce sun ga ana debe gawarwaki da dama a kasuwar da ke jihar Yobe, bayan da wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka cinna mata wuta.

Wata majiyar asibiti ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akalla mutane 34 ne suka mutu.

'Yan sanda sun ce mai yiwuwa kisan na ramuwar gayya ne kan wani mutum da 'yan kasuwar suka kashe bayan da ya yi kokarin satar saniya.

'An jefa ababan fashewa'

"Wasu gungun mutane dauke da abubuwan fashewa da bindigogi sun kai hari kan kasuwar shanu ta Potiskum," a cewar mai magana da yawun 'yan sanda Toyin Gbadegesin.

"Sun jefa ababen fashewa sannan suka rinka harbi kan mai uwa da wabi, sannan suka cinna wuta a kasuwar, inda suka kashe mutane da dabbobi da dama tare da raunata wasu, mafiya yawa dillalan shanu".

Wasu mutane ne suka toshe kofar kasuwar tare da mutane a ciki, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC.

Ya kara da cewa kasuwar - wacce 'yan kasuwa ke halarta daga kasashen Chadi da Kamaru da Nijar - an kone ta gaba daya da yammacin ranar Laraba, sannan aka kone dabbobi da dama.

Masu aiko da rahotanni sun ce harin bai yi kama da na kungiyar Boko Haram ba wacce ke kai hare-hare a yankin Arewacin kasar, ciki har da garin na Potiskum a watanni 20 da suka gabata.

Hare-hare domin satar dabbobi ba bako bane a Arewacin Najeriya.

Karin bayani