CAN ta gargadi hukumomin Najeriya a karo na karshe

Image caption Ayo Oritsejafor

Shugaban kungiyar kiristoci ta Nigeria CAN, Pastor ya yi gargadi ga hukumomin Nigeria cewa wannan ne karo na karshe da zai yi kira gare su dasu baiwa kiristoci kariya.

Shugaban kiristocin na maida martani ne game da hare- hare na baya- bayan- nan da aka kai kan wurin bautar Kiristocin a Kano, wanda yayi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

Tuni dai hukumomin tsaron Nigeria suka tsaurara matakan tsaro a sassan kasar da dama.

Pastor Oritsejafor ya ce muddin basu samu sauyi ba za su yi addu'o'i ga ubangiji domin ya nuna masu matakin da za su dauka.

Ya ce akwai dubban al'ummar krista da su ka harzuka saboda hare-haren da ake kai mu su, kuma kungiyar ta na lallashinsu tana basu hakuri.

Shugaban kungiyar Kristocin ya ce bai san abun da zai faru ba, idan hakurin 'ya'yan kungiyar ya gaza.

Ya yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da matakan da su ka dace domin kare al'ummar krista a kasar.