Ya kamata Amurka da China su mutanta juna- Hu Jintao

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da shugan China Hu Jintao

Wasu manyan jami'an gwamnatin Amurka biyu da suka hada da Hillary Clinton da Timothy Geithner sun soma tattaunawa a Beijing akan mahimman batutuwa da suka shafi tattalin arziki da kuma harkokin waje.

Mrs Clinton ta ce yayinda Kasashen China da Amurka suka kasa warware dukkanin matsalolin duniya, akwai shakkun cewar za'a iya yin hakan ba tare da hadin kai tsakanin Kasashen biyu ba

Shugaban Chinan Hu Jintao yace dole ne Kasashen biyu su girmama juna, koma da a ce akwai rashin jituwa tsakaninsu.

Tatattaunawar dai, na zuwa ne bayan da Chen Gwangchen ya bar ofishin jakadancin Amurka a Beijing.

China ta tabbatarwa Amurka cewa za'a duba lafiyar Mr. Chen tare da tabbatar da tsaron lafiyarsa data iyalinsa.

Mai bijirewa gwamnatin Chinan, Chen Guangcheng ya ce yana fargabar rayuwarsa kuma yana so ya bar China wasu sa'o'i bayan ya bar ofishin jakadancin Amurka a Biejing inda ya nemi mafaka.

Mista Chen dai ya ce ya bar ofishin jakadancin Amurka ne saboda barazanar da ake yiwa iyalansa.

Amma Amurka ta ce ba ta masaniya game da cewa ana barazana game da rayuwarsa da ta iyalansu, kuma babu lokacin da mai fafutukar ya nemi mafaka a ofishin jakadancin China.

A yanzu haka dai Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton na Beijing inda take tattaunawa da jami'an China game da harkarkokin kasuwanci da na tsaro.

Mrs Clinton dai a baya ta bayyana goyon baya a kan Mistan Chen, wanda aka yiwa daurin talala na kusan shekaru biyu.

Amma da aka tattaunawar tsakanin kasashen biyu ba ta ambato sunansa ba.

But as the talks opened she did not mention him by name.

Mrs Clinton dai a jawabinta a taron ta ce Amurka ta yi imanin cewa babu kasar da ya kamata ta hana 'yancin bil'adama sunan kuma bai dace ana hukunta wanda suka nemi a basu hakokkinsu.

Jami'an China dai a ranar Laraba, sun zargi Amurka da tsoma baki a harkokin cikin gidanta, inda su ka nemi Amurka ta nemi ahuwa saboda ajiye Mista Chen da su ka yi a ofishin jakadancin ta.

A baya dai ana ganin taron zai maida hankali ne a kan Syria da kuma Koriya ta arewa, amma batun Mista Chen a yanzu haka ya dabaibaye manufar taron.