'Yan takarar shugabancin kasar Faransa sunyi zazzafar muhawara

Hakkin mallakar hoto AP

Manyan 'yan takarar shugabancin Kasar Faransa biyu sun zargi junansu da sharara karya, a lokacin wata mahawara da suka yi a gidan talabijin din Kasar, kafin zagaye na biyu na zaben Shugaban Kasar wanda ke tafe a ranar lahadi

Anyi wata zazzafar mahawara doguwa tsakanin 'yan takarar biyu, wacce tasa ake tunanin cewar babu wanda yake kaunar juna.

Batun tattalin arzikin kasa shine ya mamaye Mahawarar

Shugaba Sarkozy ya ce ba ai masa adalci ba, da ake zarginsa da matsalolin da Kasar ke fama dasu A lokaci guda kuma sai da MR Sarkozy ya fusata inda ya ambaci abokin hamayyar tasa dangurguzu Franswa Hollande da sunan dan- karamin mai batawa mutane suna

Mr Hollande dai yace idan har aka zabe shi, to zai kasance shugaba mai adalci.