An yi artabu da masu safarar miyagun kwayoyi a Mexico

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani arbatu da aka yi tsakanin sojojin kasar Mexico da kuma masu safarar miyagun kwayoyi a kasar ya janyo asarar rayuka guda goma sha biyu a arewa masu yammacin jihar Sinaloa.

Sinaloa na daya daga cikin jihohin Mexico da ta yi kaurin suna wajen laifukan da su ka daganci ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Artabun da aka yi na baya-baya nan tsakanin masu safarar miyagun kwayoyi da kuma Sojoji a Mexico ya yi muni sosai.

Masu safarar miyagun kwayoyin dai sun yi amfani da gurneti da kuma bindigogi masu sarrafa kansu inda su kai hare-hare a kan motoci sojoji a yankin Guasave.

Sojojin suma sun maida martani ne da harbe harbe abun da kuma yasa aka rufe makarantu da shaguna.

Maharan sun nemi mafaka ne a wani Otel amma daga baya sojojin su ka kora su.

Akalla mutane goma daka cikin wadanda aka kashen a artabun fararen hula da kuma masu sarrafa miyagun kwayoyi inji gwamnatin kasar a yayinda Sojoji biyu kuma su ka rasa rayukansu.

A 'yan kwanakin nan ba'a samu yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba, saboda yaki da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi ba, kamar yadda ake samu a shekaru 2010 da kuma 2011.

Amma tashin hankalin irin wannan da ya haddasa asarar rayuka da dama ba sabon abu bane a kasar Mexico musamman ma a jihar Sinaloa inda ake ci gaba da samun irin wannan matsalar.

Akwai manyan masu safarar miyagun kwayoyi da ake neman su ruwa ajallo da ke ayyukansu a jihar, kamar su Joaquin da El Chapp da kuma Guzman.

Duk da cewa dai gwamnatin kasar na yakan kungiyoyinsu, har yanzu dai an gaggara damke su a yayinda suke cin karensu ba babbaka.