An kusa cimma burin karya Al- Qaida-Shugaba Obama

Shugaba Obama da Shugaba Karzai na Afghanistan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A wata ziyara ta ba zata zuwa Afghanistan, Shugaba Obama yace an kusa cimma burin karya Al-Qa'ida

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi jawabi ga al'ummar Kasar Afghanistan a lokacin wata ziyara ta- ba- zata da ya kai Kasar, shekara guda da kisan jagoran Kungiyar Al-Qa'ida, Osama bn Ladan.

Mr. Obama, wanda yake fuskantar wani zaben, cikin watanni shida masu zuwa, ya ce Amurka na fitowa daga karkashin duhun gajimare na yaki, amma yace dole ne ta kammala aikin da ta soma a Afghanistan

Tunda farko dai, Mr. Obama ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar dabaru na kawance, tare da Shugaban Afganistan Hamid Karzai, wacce ta fayyace dangataka ta soji data farar hula, bayan karshen aikace- aikacen kungiyar NATO a shekara ta 2014

Jim kadan bayan ziyarar Shugaba Obaman dai, wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani gida inda 'yan Kasashen waje suke zama

Akalla mutane bakwai aka kashe a harin kunar bakin waken

Wadanda suka shaida lamarin sun ce harin ya shafi kananan yara wadanda basu wuce shekaru goma ba

Karin bayani