An yi barazanar kakabawa kasasashen Sudan takunkumi

sudan
Image caption Fada tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai daura takunkumi a kan kasar Sudan da Sudan ta Kudu, in ba su daina fada, suka koma teburin shawarwari ba.

Kwamitin ya amince da wani kuduri ba tare da hamayya ba, wanda ya baiwa kasashen biyu kwanaki biyu da su dakatar da fada, su kuma shiga tattaunawa cikin makonni biyu.

A makonnin da suka wuce ne fada ya barke a wasu yankunan kan iyakar kasashen biyu, inda Sudan ta Kudu ta mamaye rijiyar mai ta Heglig, wadda ita ta fi samar wa Sudan damai.

Sudan ta ce a yanzu ta koma tura mai daga Heglig din, bayan da Sudan ta Kudu ta janye dakarunta a yan kwanakin da suka wuce.

Karin bayani