Amurka ta fitar da bayanin sirri a kan Osama bin Ladan

Wani magoyin bayan Osama bin Ladan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Obama ya ce da sauran aiki

Amurka ta saki bakwai daga cikin sama da bayanan sirri dubu shidda da dakarunta na musanman suka kwashe bayan sun kashe Osama Bin Laden.

Masu binciken da suka yi aiki akan dakardun sun ce bayanan da aka gano, sun nuna cewa Bin Laden ya gajji da sha'anin kungiyoyin jihadin da ke karkashin Alka'ida a sassan duniya da dama.

Wasu sun ce a maida hankali a kan kaiwa Amurka hari, wasu kuma sun ce akai wa Shugaba Obama hari idan ya ziyarci Afghanistan.

Bayanan sun ce an yi mahawara a kan ko a sauya wa Alka’ida suna.

Sai dai babu wani abu da ke nuna cewa Bin Laden ya samu taimako daga gwamnatin Pakistan ko kuma daga sojinta .

Karin bayani