'Ba zamu daga zaben shugaban kasa ba a Masar'

masar Hakkin mallakar hoto
Image caption Harin da aka kai a Masar

Majalisar kolin soji ta Masar tace tana nan akan bakanta na gudanar da zaben shugaban kasa.

Sanarwar na zuwa ne kwana guda bayan wasu da ba'a san ko su wanene ba suka hallaka akalla mutane 20 dake zaman dirshen a birnin Al-kahira.

'Yan kasar dadama dai na dora alhakin kisan ne akan sojin kasar.

Aysam El-Rrain dan kungiyar 'yan uwa musulmi ya ce "a bayyana ne take cewa wadannan abubuwan na faruwa akai akai, kuma a gaskiya babu dadi kuma abun tausayi ne".

Amma wani kakkakin majalisar kolin sojin ya ce yaji takaicin lamarin, ya kuma kara da cewa sojoji bazasu yi amfani da karfi ba akan masu zanga zanga.

Karin bayani