Mahara sun kashe mutane 34 a Potiskum

Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar

A Najeriya, rundunar tsaro ta JTF a Yobe ta ce akalla mutane 34 ne suka mutu da kuma dabbobi, yayinda wasu 29 suka jikkata biyo bayan harin da aka kai a kasuwar shanu dake Potuskum.

kwamandan rundunar kanal Dahiru AbdusSalam yace da maraicen jiya ne wasu mahara dauke da makamai da abubuwa masu fashewa suka kai hari a kasuwar.

Maharan sun shiga kasuwar inda suka jejjefa abubuwa masu fashewa, abinda yasa wuta ta kama a kasuwar, sannan suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.

Jami'an tsaro sun ce harin na daukar fansa ne bayan kashe wani barawo da ya je sata a kasuwar da rana a ranar laraba.

Kawo yanzu dai abubuwa sun koma yadda suke a garin na Potuskum da kuma kasuwar shanu, inda lamarin ya auku.

'An jefa ababan fashewa'

"Wasu gungun mutane dauke da abubuwan fashewa da bindigogi sun kai hari kan kasuwar shanu ta Potiskum," a cewar mai magana da yawun 'yan sanda Toyin Gbadegesin.

"Sun jefa ababen fashewa sannan suka rinka harbi kan mai uwa da wabi, sannan suka cinna wuta a kasuwar, inda suka kashe mutane da dabbobi da dama tare da raunata wasu, mafiya yawa dillalan shanu".

Wasu mutane ne suka toshe kofar kasuwar tare da mutane a ciki, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC.

Ya kara da cewa kasuwar - wacce 'yan kasuwa ke halarta daga kasashen Chadi da Kamaru da Nijar - an kone ta gaba daya da yammacin ranar Laraba, sannan aka kone dabbobi da dama.

Masu aiko da rahotanni sun ce harin bai yi kama da na kungiyar Boko Haram ba wacce ke kai hare-hare a yankin Arewacin kasar, ciki har da garin na Potiskum a watanni 20 da suka gabata.

Hare-hare domin satar dabbobi ba bako bane a Arewacin Najeriya.

Karin bayani