Labour ta taka rawar-gani a zaben Burtaniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban jam'iyyar Labour, Ed Milliband

Jam'iyyun Conservative da Liberal Democrat masu mulki a Burtnaiya sun sha kaye a zabukan kananan hukumomin da aka gudanar a sassa da dama na kasar yayinda jam'iyyar adawa ta Labour ta yi rawar gani sosai.

Masu zabe dai ba su fito sosai ba.

Ko da yake a bisa al'ada masu kada kuri'a kan yi amfani da zabukan kananan hukumomi don gasawa gwamnatin kasa aya a hannu, sakamakon zaben zai jefa gwamnatin gamin gambizar cikin damuwa.

Jam'iyyar Labour dai za ta yiwa sakamakon kallon alamun komawarta kan kujerar mulki.

Mai yiwuwa 'yan jam'iyyar Conservative su nemi jam'iyyar ta kara bin manufofin ra'ayin rikau yayin da 'yan jam'iyyar Liberal Democrat za su kara nesanta kansu da gwamnatin.