An yi dauki ba -dadi a kusa da ma'aikatar tsaron Masar

Masu zanga zanga a Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Masar

Dakarun tsaro a Masar sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da kuma ruwan zafi domin kora daruruwan masu zanga zangar dake jifa da duwatsu baya daga Ma'aikatar tsaro a Alkahira.

Mutane fiye da 50 ne aka bayar da rahoton sun samu rauni sannan an kama wasu da yawa.

Tashin hankali ya barke bayan da masu zanga zanga suka yi watsi da kashedin soji da yawa na kada su kuskura su tinkari ma'aikatar a inda wasu makasan da ba a tantance ba suka hari masu zanga zanga a ranar laraba, inda suka kashe kusan 20.

Masu zanga zangar sun zargi majalisar mulkin soji da shirya kai harin.Tashin hankalin ya faru ne makunni kawai kafin zaben Shugaban kasa -- wanda bayansa majalisar mulkin sojin ta ce za ta mika mulki.

Karin bayani