An hallaka mutane 3 a Maiduguri

Maiduguri
Image caption Maiduguri

Rahotanni daga jihar Borno sun ce, mutum 3 sun hallaka yayin da wasu 4 su ka ji raunuka, a lokacin taho-mu-gamar da aka yi tsakanin jami'an rundunar tsaro ta hadin gwiwa da wasu 'yan bindiga.

An yi musayar wutar ce a unguwar Sabon Layi a Maiduguri, babban birnin jahar Bornon.

Rundunar tsaron ta ce ta kama biyu daga cikin 'yan bindigar.

Rahotanni kuma daga karamar hukumar Riyom a jihar Plateau sun ce, ana ci gaba da zub da jini da kuma kona gidaje, inda lamarin ya yi kamari a 'yan kwanakin nan.

Hukumomi sun tura karin jami'an tsaro zuwa yankin, amma dai ana ci gaba da zaman dar-dar saboda halin rashin tabbas.

Karin bayani