Japan za ta rufe na'urar sarrafa nukiliya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutanen da ke adawa da makamashin nukiliya

A ranar Asabar ne Japan za ta rufe na'aurarta ta karshe mai sarrafa makamashin nukiliya; hakan kuma zai sa ta kasance babu wutar lantarkin da ake samu daga makamashin nukiliya a karo na farko a shekaru arba'in.

Na'urar da ke tashar nukiliya ta Tomari a arewacin Japan, ita ce ta karshe a cikin na'urori fiye da hamsin din da aka rufe don yin gyare-gyare tun bayan girgizar kasar da ta haddasa bala'in tashar nukiliya ta Fukushima a bara.

Daruruwan Japanawa ne dai suka yi jerin gwano, suna nuna wasu alluna da ke cewa, 'ba mu ba makamashin nukiliya', a lokacin da ake bikin rufe na'urar sarrafa makamashin nukiliyar.

Mutanen, wadanda suka taru a wani wajen shakatawa da ke birnin Tokyo, sun ce ba su damu da gargadin da gwamnati ta yi cewa za a fuskanci matsalar rashin wutar lantarki sanadiyar rufe na'urar ba.

Gwamnatin kasar ta Japan dai za ta so ta ci gaba da samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin nukiliya amma kuma kananan hukumomin kasar sun ki amincewa a sake bude tashohin nukiliyar.

Karin bayani