An hallaka mutane 23 a Mexico

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane na kallon jinin da ya fallatsa bayan an kashe wasu mutane a Mexico

An kashe akalla mutane ashirin da uku a wani yanayi maras kyawun gani a birnin Nuevo Laredo na Mexico wanda ke kan iyakar kasar da Amurka.

An samu gawarwakin tara wadanda ga alamu an azabtar da su a rataye a jikin wata gada, yayin da sa'o'i kalilan bayan nan aka gano wadansu gawarwakin goma sha hudu wadanda aka yankewa kawuna a wata mota.

An dai tsinci kawunan a cikin wasu akwatunan kula na ruwa wadanda aka yar a kofar ofishin magajin garin birnin.

Wata wasika da aka samu a kusa da gawarwakin ta ce mutanen 'yan kungiyar da ke safarar miyagun kwayoyi ce, kuma abokan gabar su ne suka kashe su.

Wasikar ta kuma bayyana cewa da sannu za a ci gaba da kashe karin wasu 'yan kungiyar da aka kashe din.

Kafafen yada labaran Mexico dai sun ce da alama wannan kisan ramuwar gayya ce da masu safarar miyagun kwayoyi ke yi a yunkurinsu na samun iko wajen fitar da kwayoyin zuwa Amurka.

Hukumomi a jihar dai sun gudanar da taron gaggauwa game da batun, inda suka yanke shawarar aikewa da karin jam'ian tsaro zuwa yankin.

Karin bayani