Harin bam a birnin Aleppo na Syria

Tashin hankali a Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tashin hankali a Syria

Masu fafutuka a Syria sun ce, akalla mutane 5 sun hallaka, a lokacin da wani bam ya fashe a birnin Aleppo na arewacin kasar.

Wasu mutanen kuma sun jikkata a Damascus, babban birnin kasar ta Syria, yayin fashewar wasu bama-bamai biyu.

Fashe fashen sun biyo bayan yinin da aka kwashe ne ana tashin hankali a Syriar, inda mutane akalla 30 suka rasa rayukansu, a cewar 'yan gwagwarmaya - duk kuwa da kasancewar tawagar masu sa-ido na majalisar dinkin duniya a kasar.

Wakilin BBC Jonathan Head ya ce, ko da majalisar dinkin duniya ta tura cikakiyar tawagar masu sa ido zuwa Syriar, da wuya ta iya maido da zaman lafiyar da zai sa a soma duk wata sasantawar siyasa tsakanin bangarori.

Karin bayani