Hadari ya hallaka mutane a Zamfara

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriya akalla mutane 8 sun rasa rayukansu kuma dayawa sun jikkata, sakamakon iska mai karfin gaske da ke tafe da ruwa a jahar Zamfara.

Shaidu sun ce daruruwan gidaje sun rushe sakamakon hadarin.

A garin Maradun kawo yanzu hukumomi sun tabbatar da rushewar gidaje akalla 500.

Garuruwa akalla bakwai ne lamarin ya shafa a jahar ta Zamfara.

Daruruwan iyalai sun nemi mafaka a gidajen 'yan uwa da abokan arziki, wadanda Allah ya yiwa gyadar dogo.

A ranar Litinin da ta wuce kimanin gidaje dari ne suka lalace a jahar Sakkwato mai makwabtaka da Zamfarar, sakamakon iska mai karfin gaske da ke tafe da ruwa.

Karin bayani