Ana zabubuka a Turai

Zaben shugaba kasa a Faransa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zaben shugaban kasa a Faransa

Ana gudanar da zabubuka a kasashe da dama na Tarayyar Turai, a daidai lokacin da ake fama da matsalar kudade a yankin Euro.

A Faransa masu jefa kuri'a za su yi zabe ne tsakanin shugaba mai ci a yanzu, Nicolas Sarkozy, da abokin hamayyarsa na bangaren gurguzu, Francois Hollande.

Ra'ayoyin mutanen biyu ya sha bambam sosai a kan yadda za a bullo wa matsalar kudaden.

A kasar Girka ana zaben majalisar dokoki ne, bayan an kwashe shekaru biyu ana aiwatar da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati marasa farinjini.

A Italiya ana kada kuri'a a zaben kananan hukumomi, wanda gwaji ne na tasirin gwamnatin da ta karbi mulki daga Silvio Berlusconi watanni shida da suka gabata.

A Jamus kuma, a jahar Schleswig-Holstein, hadin gwiwar jam'iyyu masu matsakaicin ra'ayin rikau, masu goyon bayan shugabar gwamnati Angela Merkel, suna kokari ne su ga basu rasa rinjayen da suke da shi a sabuwar majalisar dokokin kasar ba.

Duk wani kayen da zasu sha zai janyo cikas wajen sake zaben Angela Merkel a shekara mai zuwa.

Karin bayani