Ana zaben shugaban kasa a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mutum na kada kuri'arsa a zaben shugaban kasar Faransa

An bude rumfunan zabe don kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Faransa, inda Nicolas Sarkozy ke fafatawa da Francois Hollande.

Batun tangaltangal din tattalin arziki da kuma bambancin mahangar 'yan takarar dangane da matsalar kasashe masu amfani da kudin euro ne suka kankane yakin neman zabe.

Mista Hollande dai na da burin sauya fasalin yarjejeniyar da Shugaba Sarkozy ya taimaka aka cimma don magance matsalar bashin da ake bin kasashen.

A Girka ma ana gudanar da zaben majalisar dokoki mai matukar muhimmanci, wanda ake yi wa kallon kuri'ar raba-gardama kan matakan tsuke bakin aljihun da aka dauka don samun tallafi daga cibiyoyin kudi na duniya.

Kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar da aka gudanar gabanin zaben na yau ta nuna cewa 'yan kasar ta Girka sun sha alwashin koyawa manyan jam'iyun kasar darasi, saboda amincewar da suka yi da shirin ceto tattalin arzikin da manyan cibiyoyin kudin suka gabatar.

Zabukan biyu dai ka iya yin tasiri sosai a kan makomar kudin euro.

Karin bayani