Francois Hollande ya lashe zaben Faransa

Francois Hollande, sabon shugaban Faransa Hakkin mallakar hoto
Image caption Francois Hollande, sabon shugaban Faransa

Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy, ya amince ya sha kaye bayan an kammala zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

Sarkozy ya ce, ya kira abokin karawarsa, Francois Hollande na jam'iyyar gurguzu, ya taya shi murnar zama sabon shugaban kasar.

Bayan an kammala zaben an ce Francois Hollande ya sami kashi 52 cikin dari na kuri'un, yayin da shi kuma Nicolas Sarkozy ke da kashi 48 cikin 100.

Yanzu dai Francois Hollande zai zama dan jam'iyyar gurguzu na farko da ya lashe zaben shugaban Faransa a cikin shekaru sha bakwai.

Shi kuma Nicolas Sarkozy zai zama shugaban kasa mai ci da ya sha kaye a zabe tun shekarar 1981.

Tuni dai 'yan jam'iyyar gurguzu suka ce abinda zasu fi baiwa muhimmanci shi ne sake duba yarjejeniyar Tarayyar Turai akan tattalin arziki.

Can kuma a kasar Girka, ra'ayoyin wadanda suka kada kuri'a a babban zaben da aka yi yau na nuna cewa, jam'iyyun siyasar da suke adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati mai tsaurin gaske, sun samu kuri'u da dama, fiye ma da jam'iyyun da suka yi kaka-gida a fagen siyasar kasar tun shekara da shekaru.

Karin bayani