Nijar na bukatar agajin abinci

Matsalar yunwa a Nijar
Image caption Matsalar yunwa a Nijar

Wasu manyan jami'an majalisar dinkin duniya suna ziyara a jamhuriyar Nijar, domin duba halin da kasar ke ciki ta fuskar abinci

Jami'an sun hada da Darekar hukumar samar da abincin majalisar, WFP ko PAM, da shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira.

Kimanin mutane miliyan shidda ne ke fuskantar karancin cimaka a Nijar din.

Gobe Litinin jami'an majalisar dinkin duniyar zasu gana da mahukuntan Nijar din, ciki har da shugaba Issoufou Mahamadou, domin duba yadda za a taimaka wa kasar ta fuskar cimaka.

Bangarorin biyu kuma za su tattauna a kan makomar dubban 'yan gudun hijirar Mali da ke zaune a kasar ta Nijar.

Karin bayani