Obama ya kaddamar da yakin neman zabe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barack Obama

Shugaba Obama na Amurka ya kaddamar da yakin neman sake zabensa a watan Nuwamba da gagarumin gangami a jihohin Ohio da Virginia.

Mista Obama ya shaidawa magoya bayansa cewa a bisa shugabancinsa Amurka ta farfado daga koma-bayan tattalin arzikin da ta fada.

Ya kuma yi gargadin cewa abokin adawarsa na jam'iyyar Republican, Mitt Romney, na so ya maimaita kurakuran da aka tafka a baya, na sassautawa mawadata haraji da kuma rage yawan kudin da ake kashewa don amfanin talakawa:

''Kalubalen da muke fuskanta yanzu haka, kuma kalubalen da muka yi ta fuskanta a shekaru goman da suka wuce, shi ne cewa zafin nema ba ya kawo samu''.

Karin bayani