Girka: Antonis Samaras ya gaza kafa gwamnati

Image caption Aleksis Tsipras

A kasar Girka an nemi Jagoran masu ra'ayin kawo sauyi ya kafa sabuwar gwamnati bayan takwaransa na masu matsakaicin ra'ayin rikau ya ce ya gaza kafa gwamnatin kawance.

Jam'iyyar Syriza dake karkashin jagorancin Alexis Tsipras tana son kafa gwamnatin da za ta yi wa tsi da matakan tsuke bakin aljihu da aka tilasta wa kasar Girkar amfani da su ne a matsayin hanya mafificiya ga kangin tattalin arzikin da ta afka.

Jam'iyyar New Democracy ce ta masu matsakaicin ra'ayin rikau ta cinye mafi rinjayen kuri'u a zaben da aka yi ranar Lahadi, jagoranta Antonis Samaras ya ce ya yi bakin iyakar kokarinsa na kafa gwamnati, amma ya gaza.

Karin bayani