Girka: NDC ta gaza kafa gwamnati

Shugaban jam'iyyar NDC ta masu matsakaicin ra'ayin rikau a kasar Girka, Antonis Samaras ya ce ya gaza a kokarinsa na kafa gwamnatin hadin gwiwa.

Ya bayyana hakan ne, sa'o'i kadan bayan an ba shi izinin kafa gwamnati a matsayin jagoran jam'iyyar da ta fi yawan wakilai a sabuwar majalisar dokokin kasar.

Ana danganta jam'iyyar ta NDC da matakin tsuke bakin aljihun da aka dauka a kasar ta Girka masu tsaurin gaske.

A yanzu jagoran jam'iyyar kawance ta Syriza ta masu ra'ayin sauyi, kawancen da yayi adawa shirin baiwa kasar tallafi, shi ne zai gwada sa'arsa.

Sai dai kuma wakilin BBC a Athens ya ce ana tsammanin shi ma, zai ji jiki, kafin ya iya samun adadin kujerun da ake bukata, lamarin da zai iya janyo a ci gaba da jayayyar siyasa ta lokaci mai tsawo.