Iyaye mata sun fi shan wahala a Nijer

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption mata a Nijer

Kungiyar ba da agaji ta Save The Children ta ce a yanzu ta kimanta Nijer dake yammacin Afrika a matsayin kasar da Iyaye Mata suka fi shan wahala a duniya.

A rahoton ta na shekara-shekara na kwatanta ha lin da Iyaye Mata suke ciki a duniya, Kungiyar ta ce Nijer ta maye gurbin Afghanistan a wannan sahu.

A halin yanzu dai Nijer din tana fuskantar matsalar karancin abinci sakamakon farin da ake fuskanta a yankin Sahel.

Karin bayani