Vladimir Putin ya sha rantsuwar kama aiki

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Vladimir Putin

A yau litinin ne Mr. Vladimir Putin ya sake komawa kan kujerar shugabancin Rasha, bayan an rantsar da shi a karo na uku a yayin wani biki a Moscow.

Ya sha rantsuwar kama shugabancin kasar ne a fadar Kremlin.

A jawabin karbar mulki, Mr. Putin ya ce zai tabbatar da samun cigaban kasar.

Sai dai wasu mutane kusan dari sunyi bore a wajen fadar don nuna rashin amincewarsu da shan rantsuwar Mr. Putin.

Mista Putin na fuskantar matsalolin da suka hada da na bijirewa daga wasu mutanen kasar da kuma koma bayan tattalin arziki.

A 'yan watannin da suka gabata dai an gudanar da manya-manyan tarukan zanga-zanga a titunan Moscow, tsarin siyasar da ya assasa kuma ya fara nuna alamun baraka, sannan ana sa ran tattalin arzikin kasar zai fara fuskantar koma-baya.

Karin bayani