Jami'in leken asiri ya yaudari Al Qaeda

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kabul CIA

Rahotanni daga Amurka sun ce, mutumin da aka shirya makarkashiyar kai harim bam wanda aka sanya a cikin dan kampai, shirin da Amurkar da kawayenta suka ce sun wargaza ma'aikaci ne na wasu hukumomin leken asiri.

An rawaito jami'an Amurkar a yanzu suna fadin cewa mutumin da aka shirya zai kai harin, yana yi wa hukumomin leken asiri ne na CIA da Saudiyya aiki a lokacinda aka ba shi bam din.

Bam din wanda ya mika ga Amurkawan an bayyana cewar irin wanda al-qaeda ne ta yi makarkashiyar kai hari da shi a shekara ta dubu da tara, amma ya zarce shi ta fuskar inganci.

Wanda ya ke tseguntawa hukumomin Saudiyyar da CIA bayana sirrin na kasar Saudiyya cikin koshin lafiya.

Haka kuma ta makarkashiyar ne aka samu bayanai da suka sa Amurka suka kai harin Jirgin saman dake sarrafa kansa wanda ya kashe wani jigon Alqaeda a Yemen.

Karin bayani