An fara gabatar da shaidu a shara'ar Breivik

Hakkin mallakar hoto Reuters

An soma jin bahasi daga wadanda suka tsira bayanda dan kasar Norway Anders Behring Breivik ya kashe mutane a wani tsibiri a kusada Oslo.

An dai saurari shari'ar da ake yiwa Anders Behring Breivik ne, mutumin da yayi ta ihu na jin dadi a lokacin da ya yi harbin da ya kashe mutane 69 a tsibirin Utoeya na kasar Norway a watan Julin daya gabata.

Masu gabatar da kara sun ce Mr Breivik ya kashe mutane 77 ne, 69 daga cikin su ya kashe su ne a wani wurin sansanin matasa a Utoeya, yayin da kuma ya hallaka mutane takwas a wani harin bomb daya kai a Birnin Oslo a ranar 22 na watan Yulin shekarar data gabata.

A lokacin da take gabatar da shaida a gaban kotun, shugabar matasa na jam'iyar Labour Tonje Brenna ta ce ta ji yadda Mr Breivik din ke ta ihu jin dadi a lokacin da yake kisan.

Shima wani mutum daya bada shaida gaban kotun ya ce yaga yadda Breivik yayi ta luguden wuta akan wasu mutane dake iyo inda suke kokarin neman su tsira.

Shi dai Mr Breivik ya amince cewa ya aikata kisan, sai dai ya ce shi kam bai aikata wani laifi ba.

Sai dai shi Breivik di nayyi ta kokarin nuna cewa lafiyar kalau don tabbatar da cewa ya aikata wannan danyen aiki ne don ya cimma burinsa.