An soma taron tattalin arzikin duniya kan Afrika

taron Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Taron tattalin arziki

An soma taron tattalin arzikin Duniya kan Afrika yau a Addis Ababa babban birnin Ethiopia.

Wannan shi ne karon farko da ake gudanar da taron a kasar -- wadda ke da muhimmanci a matsayin wani babban misali na daya daga cikin kasashen nahiyar dake samun ci gaban tattalin arziki cikin hanzari.

Hasashen tattalin arzukin nahiyar Afrika dai ya ci gaba da kasancewa mai haskakawa a wani lokacin da sauran duniya ke fuskantar manyan kalubalen siyasa da na tattalin arziki.

Karin bayani