Sojin Libya sun hana mamaye ofishin Prime Minista

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Belhadj wakilin juyin juyi hali na Libya

Dakarun sojin kasar Libya sun hana masu bore dauke da makamai mamaye hedi kwatar Prime minista a babban birni kasar Tripoli.

Masu kai harin tsofaffin yan tawaye ne dake wajen babban birnin Tripoli wadanda sukayi yaki don hambararar da shugaba colonel Muammar ghaddafi shekrara da ta gabata.

Tsofaffin yan tawayen na bukatar diyyar da gwamnatin tayi musu alkawari.

Hukumomi sun ce an kashe wani mamba na dakaraun sojin wasu mutane uku kuma sun jikkata.

An ambanto Kakakin Prime Ministan yana cewa amfani da makamai wajan neman biyan bukatu ba abune da za'a lamunta ba.

Karin bayani