An mayar da Ayo Salami kan kujerarsa

Ayo Salami
Image caption A yanzu hankali zai karkata kan shugaba Goodluck Jonathan

Bayanan da BBC ta samu daga majalisar kula da al'amuran shari'a ta Najeriya NJC na cewa hukumar ta yanke matsayin mayar da Ayo Salami kan kujerarsa ta shugabancin kotun daukaka kara. .

An dai dakatar da mai shari'a Salami ne sakamakon wata takaddama da ta shiga tsakaninsa da tsohon shugaban kotun kolin kasar mai shari'a Aloysious Katsina Alu.

Wata majiya a NJC ta shaida wa BBC cewa, an yanke shawarar mai da Ayo Salami bisa kan kujerarsa ta shugabancin kotun daukaka karar ne a ranar Alhamis, a karshen wani taron majalisar da ta kammala a Abuja.

Majiyar ta ce an cimma matsayar ne bayan an tattauna a kan rahoton wani kwamiti da majalisar ta kafa karkashin jagorancin mataimakiyar shugabar majalisar mai shari'a Aloma Mukhtar.

Majiyar ta kuma kara da cewa an yi muhawara a kan rahoton inda daga karshe mambobin majalisar suka kada kuri'a a kan a mayar da shi ko a'a, kuma masu son a mayar da shi suka yi rinjaye.

A yanzu dai abinda ya rage shi ne za a mika matsayar da hukumar ta cimma ga shugaban Najeriya Goodluck Jonathan domin ya bada umarnin mayar da shi bisa mukaminsa.

Asalin rikicin

Rikicin da ya taso tsakanin mai shari'a Ayo Salami da tsohon cif Jojin Najeriya Aloysius Katsina Alu dai ya janyo dambaruwa mai zafi da ta kawo rarrabuwa tsakanin masana harkar shari'a a kasar.

Rikicin ya kuma kara bayyana irin zarge-zargen cin hanci da rasahwa da ake yiwa alkalai da lauyoyi a kasar, batun ya kai a lokacin aka ambato shugaban kungiyar lauyoyi na kasa Barista JB Daudu yana cewa sashen shari'a na Najeriya "ya zama tamkar na sayarwa", idan kana da kudi za ka samu duk irin shari'ar da kake so.

Rikicin dai ya samo asali ne a lokacin da cif jojin Najeriya na lokacin Aloysious Katsina Alu ya nemi da ya nada mai shari'a Salami a matsayin alkalin kotun koli, shi kuma Salami ya ce baya so.

A cewarsa 'Katsina Alu yana son ya raba shi da kujerarsa ne domin ya ki ya yarda da sanya bakin da cif jojin ya ke son yi a kan hukuncin shari'ar zabe da aka yi ta jihar Sokoto dake arewacin kasar'.

A baya dai an nemi Ayo Salami da ya nemi afuwar Katsina Alu bisa zargin da ya yi masa kafin a mayar da shi kan mukaminsa.

Hankali dai zai karkata ne ga fadar shugaban kasa domin ganin matakin da za ta dauka kan matsayar da majalisar kula da al'amuran shari'ar kasar ta dauka na a mayar da Justice Ayo Salami kan kujerarsa ta shugabancin kotun daukaka kara ta Najeriya.

Karin bayani