Ana fama da bala'in yunwa a Sudan

sudan

Asalin hoton, msf

Bayanan hoto,

Wasu mata a Sudan

'Yan tawayen dake fafatawa da gwamnatin Sudan wadanda ke arewa daga kan iyakar kasar Sudan da kuma Sudan ta Kudu, sun ce fararen hula a yankin na fuskantar bala'in yunwa.

Malik Agar wanda shine shugaban 'yan tawayen SPLM a arewa ya shaidawa BBC cewar fiye da mutane 2000 a jihar Blue Nile na matukar bukatar abinci.

A cewarsa a yanzu haka, kananan yara da tsaffi sun soma mutuwa sakamakon 'yunwa, a don haka ya bukaci kasashen duniya su kawo dauki.

Wakilin BBC na Afrika Martin Plaut ya ce "akwai matsin lamba akan a tura abinci a yankunan da ake tashin hankali , kooda gwamnati bata amince ba, kamar yadda lamarin yake lokacin da Sudan ta Kudu tayi ta yaki don samun 'yancin kanta".

A cewar shugaban 'yan tawayen Malik Agar, mahukunta a Sudan sun tsohe hanyoyin kaiwa jama'a agaji.