Tattalin arzikin kasashen EU zai yi kasa

Wurin binciken tsaro

Kungiyar tarrayar Turai wato EU ta bayyana cewar tattalin arzikin kasashen dake amfani da kudin Euro zai kara yin kasa a bana, kuma kasar Spain na daga cikin kasashen dake fuskantar babbar matsala musamman a bangaren harkokin banki.

Gwamnatin Spain dai na shirin fitar da wani tsarin sake fasalin tattalin arzikinta, ta yadda za a tilastawa bankuna su ware wasu kudade, a matsayin rigakafi daga irin hasarar da suke tafkawa.

A birnin Brussels kwamishinan kula da tattalin arziki Turai, Olli Rehn yace, dole ne sai mun cimma matsaya akan batun samun daidaito da kuma bukatar bukansar tattalin arziki, daga nan kuma sai muyi garan bawul a manufofinmu na tattalin arziki.