An shafe daren jiya ana lugudan wuta a Syria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojan Syria

Sojojin gwamnati a kasar Syria sun shafe daren jiya suna lugudan wuta a birnin Homs abinda 'yan adawa masu fafutuka suka bayyana cewar shi ne mafi muuni a cikin makonni.

An ajiye wakilai goma sha-daya masu sa ido na majalisar dinkin duniya yanzu haka a birnin na Homs don su yi kokarin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a can.

To amma wakiliyar BBC dake tafiya da wakilan na majalisar dinkin duniya ta ce suna da jan aiki a gabansu, saboda karya yarjejeniyar da dukkan bangarorin suke yi.

Gwamnan birnin Ghassan Abul-Lal ya gaya wa BBC cewar masu sa idon na majalisar dinkin duniya suna tsawata wa 'yan adawar wadanda ya zarge su da laifin cigaba da kai harin.

Karin bayani