Girka: Ana kokarin kafa gwamnati

Shugabannin Girka Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban kasar Girka, Karolos Papoulias, ya fara yunkurin kafa wata gwamnatin gaggawa domin kaucewa shirya sabon zabe, sakamakon kasa samun wanda ya yi nasara a zaben ranar Lahadin da ta wuce.

Mista Papoulias ya gayyaci shugabannin dukkan manyan jam'iyyun kasar wajen wani taro ranar Asabar.

Tsoma bakin nasa dai ya zama tilas ne bayan da a karo daban-daban ko wacce daga cikin manyan jam'iyyun kasar uku ta kaza kafa gwamnati.

Daya daga cikin shugabannin jam'iyyun, Evangelos Venizelos, ya ce ya mayar da izinin da aka ba shi na kafa gwamnati, bayan da hakan ya ci-tura.