Majalisar dinkin duniya tayi tur da hari a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption harin bam a Syria

Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya ya yi Allah wa dai da wasu hare-hare biyu na kunar bakin-wake wanda ya hallaka mutane da dama a Damascus babban birnin kasar Syria.

Wakilan kwamitin sun yadda cewar shirin samar da zaman lafiyar a Syria yana fuskantar matsaloli, amma sun na ce a kan cewar ba a da wani za bi.

Jakadan Syriar ya gaya wa kwamitin sulhun cewar 'yan ta'adda ne suka kai wannan hari.

Bashar Ja'afari ya zargi kasashen waje da laifin baiwa kungiyoyin dake gwagwarmaya kudi da makamai.

Ya dora laifin a kan wasu mayaka 'yan kasar waje masu alaka da kungiyar al-qaeda ga karuwar hare-haren da ake kaiwa, ya kuma ce kama ta ya yi majalisar dinkin duniya ta dauki matakin dakatar da su.

Karin bayani