Kungiyar bada agaji ta yi gargadi kan gubar dalma

Image caption Goodluck Jonathan

Kungiyar ba da agaji ta Medicine Sans Frontiers ta sake yin kashedi ga hadarin dake tattare da gubar dalma da ake samu a yankin arewacin Najeriya.

Kungiyar ta ce daruruwan yara sun mutu saboda haduwa da gubar dalmar a jihar Zamfara tun lokacin da aka ga no matsalar shekaru uku da suka wuce wadda aka danganta ta da kurar dake tashi a yayinda ake hakar zinari.

Kungiyar tace akwai mutane dubu hudu da suka kamu da gubar dalmar, har yanzu kuma ba su samu magani ba.

Gwamnatin kasar dai ta ce tana kokarin bin hanyoyin da za ta kare mazauna yankin da suke fuskantar matsalar hako dalmar.

Karin bayani