Sarki Abdallah ya kori mai bashi shawara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sarki Abdullah na Saudi Arabia

Sarki Abdallah na Saudi Arabia ya kori daya daga cikin masu bashi shawara mafi ra'ayin rikau, wanda baya boye matsayinsa akan sukar lamirin matakin sassauta dokar hadauwar maza da mata a wuraren jama'a.

Babu wani dalili da aka bayar na korar Sheik Abdelmohsen al-Obeikan.

Korar tasa dai ta zo ne kwanaki kadan bayan da malamin ya yi suka akan abin da ya kira shirin da wasu masu-fada-a-ji ke yi na gurbata al'ummar musulmi ta kokarin sauya matsayin mata na hakika.

Shi dai Sarkin na Saudiyya wanda ke kawo sauye-sauye a tsarin kasar a 'yan shekarun baya-bayan nan ya goyi bayan sassauta wasu tsauraran fatawowin musulunci.

Da ma Sheik Abdulmohsen ya yi kaurin suna akan wata fatawa da ya taba bayarwa wacce ta ce maza da matan da ba 'yan uwan juna ba na iya haduwa a waje guda idan namijin ya sha nonon matar.

Karin bayani