'Sudan Ta Kudu ta janye 'yan sandanta daga Abyei'

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan ta Kudu ta janye 'yan sandanta daga yankin Abyei da ake takaddama tsakaninta da Sudan akansa.

Dukkanin kasashen biyu na ikirarin mallakar yankin na Abyei wanda ke da arzikin kasar noma da mai.

Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya, Martin Nesirky, ya ce kimanin 'yansanda 700 ne na Sudan ta Kudun suka koma kasarsu.

Shugabar Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay, ta ce harin sama da sojin Sudan suke kai wa Sudan ta Kudu na iya zama laifukan yaki.

Ms Pilya wadda ta je babban birnin Sudan ta Kudu, Juba ta yi Alla-wadai da abin da ta kira harin takala akan yankunan fararen hula.

Karin bayani