Ecowas: an samu cikas a Mali

Wani taron shugabannin ECOWAS Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wasu wakilan musamman na kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ko CEDEAO sun bar Mali bayan sun gaza cinma yarjejeniya a kan wanda ya kamata ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya.

A watan jiya ne aka nada shugaban kasar na rikon kwarya, Dioncounda Traore, bayan da shugabanin juyin mulki suka amince su sauka daga mulki.

ECOWAS na cewa ya kamata a bar Mr Traore ya ci gaba da shugabanci bayan wa'adin mulkinsa na kwana arba'in ya kare.

A halin da ake ciki, kasar Malin ta rabu biyu, inda 'yan tawayen Azibinawa ke rike da arewacin kasar.