Uganda: an kama wani kwamandan LRA

Caeser Achellam, wanda aka kama, Hakkin mallakar hoto Reuters James Akena

Rundunar sojan Uganda ta ce ta cafke wani baban kwamanda na kungiyar 'yan tawaye ta LRA, kungiyar da ta ke ta aikata kisa, tana kuma sace jama'a a yankin gabashi da na tsakiyar Afrika, cikin shekaru ashirin da suka gabata.

Wakiliyar BBC ta ce, rundunar sojan Ugandan ta ce ta kama Caeser Achellam, kusa a kungiyar LRA ne a wani kwanton bauna, a gabar kogin Mbu, a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Ana neman jagoran kungiyar ta LRA, Joseph Kony ne ruwa-a-jallo, bisa tuhumar aikata laifukkan yaki.

Dakarun sojan Amurka na bada taimako ga dakarun sojan Uganda da Sudan da na jamhuriyar Dimoradiyar Congo da ma na ta Afrika ta tsakiya a farautar da suke yi ta Mista Kony.