Mexico: an gano gawarwaki 49

Jami'an tsaron Mexico Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumomi a Mexico sun gano wasu gawarwaki arba'in da tara na mutanen da aka yi wa gunduwa gunduwa, aka kuma jibge a kan wata babbar hanya, kusa da garin Monterrey dake arewacin kasar.

Jami'an tsaro sun ce an daddatsa gawarwakin, aka guntule hannayensu, ta yadda da wuya a iya gane ko su wanene.

Hukumomi sun dora alhakin kisan a kan matsananciyar gabar da ake yi tsakanin wasu kungiyoyi biyu masu safarar miyagun kwayoyi- wata wasika da aka bari kusa da gawarwakin na cewar, 'yan kungiyar Zetas ne suka aikata kisan.

Wannan shi ne na baya baya a jerin kashe kashen da ake aikatawa a arewacin Mexico, inda kungiyoyi masu safarar miyagun kwayoyi ke jayayya da juna a yunkurin karbe iko da hanyar fasakwaurin miyagun kwayoyi cikin Amurka.