Ana tattaunawa tsakanin jam'iyyun Girka

girka Hakkin mallakar hoto a
Image caption Tattaunawa tsakanin 'yan siyasar Girka

A yau shugaban kasar Girka zai yi kokari na karshe ya shawo kan wasu jam'iyyun siyasar kasar a kafa gwamnatin gaggawa ta rikon kwarya, ta yadda Girka zata kauce gudanar da sabbin zabuka.

Daya daga cikin jam'iyyu hudun da aka gayyata wajen tattaunawar-- wato jam'iyyar Syriza, mai ra'ayin rikau ta ce sam baza ta je ba, sabilida baza ta marawa duk wani kawance da ke goyan bayan matakan tsuke bakin aljuhun gwamnati ba---- tsarin da yawancin masu kada kuri'a suka ki yadda da shi a zaben da akai makon jiya.

Shi dai shugaban kasar Girka (Karolos Papoulias)yayi ta kokarin ganin ya shawo kan mambobin wasu jam'iyun siyasun kasar na su kafa gwamnatin gaggawa saboda kasar ta kaucewa gudanar da wani zabe.

Jam'iyar Syriza ta masu ra'ayin rikau wanda ke cikin jam'iyu 4 da aka gayyata domin a tattauna dasu ta ki amsa gayyatar inda ta ce ba zata shiga duk wani hadin guiwa ba dake goyon matakan tsuke bakin aljihu, bayan da akasarin jama'ar kasar suka kada kurri'ar 'kin amincewa da shirin a makon jiya.

Nikos Pappas direkta ne a ofishin shugaban jam'iyar Syriza , ya kuma shaidawa BBC cewa kudaden da aka samu rance ba za'a yi amfani dasu ba wajen taimakwa talakawan kasar Girka.

Karin bayani