'NATO ta kashe fararen hula 72 a Libya'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani hari da NATO ta kai a Libya

Wani sabon binkice game da kare hakkin dan adam ya nuna cewa dakarun kungiyar tsaro ta NATO sun kai wani hari ta sama a kasar Libya wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla fararen hula saba'in da biyu.

Rahoton ya nuna shaidun da ke cewa an kashe fararen hular ne a hare-hare guda takwas da NATO ta kaddamar.

Sai dai abin da ya fi damun kungiyar kare hakkin dan-Adam ta Human Rights Watch shi ne ba a ma mayar da hankali a kan kashe wadannan mutane ba.

NATO ta hakikance cewa ta dauki kwararan matakai na ganin cewa ba a kashe fararen hula da yawa ba.

Biyan diyya

Ta kara da cewa ba za ta dauki alhakin kai hare-haren ba tun da dai ba ta da wasu jami'ai a kasa da za su tabbatar cewa an kashe fararen hular.

Rahoton ya ce duk da haka ya kamata NATO ta gudanar da bincike a kan lamarin kuma idan ta kama ta biya diyya ga iyalan da suka rasa 'yan uwansu a hare-haren.

NATO dai ta ce ya rage ga kasar Libya idan tana son a gudanar da binciken, kuma, a cewarta, a shirye take ta bayar da hadin kai.

Karin bayani