Falasdinawa sun daina yajin cin abinci

palasdinawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu Palasdinawa a gaban gidan kaso

Falasdinawan da ke zaman wakafi a Isra'ila sun amince su kawo karshen yajin cin abincin da suke yi, bayan wata yarjejeniyar da Masar da Jordan suka taimakawa aka cimma.

Fursononi dubu-daya da dari shidda ne ke yajin cin abincin da aka fara a tsakiyar watan Afrilu.

Fursunoni Falasdinu dubu daya da dari shida ne wato kimanin kashi daya cikin ukun fursunonin da Isra'ila ke tsare da sune, su ka shiga yajin cin abincin a watan da ya gabata domin kalubalantar shirin Isra'ila na tsare fursunoni ba tare da an yi musu shari'a ba da kuma halin da suke ciki a gidan kaso.

Sun dai bukaci a kara musu lokacin da zasu rika ganawa da iyalansu.

Fursonin biyu da su ka fara yajin cin abincin a yanzu haka sun kai kwanaki 77 suna Azumi.

Yajin cin abincin da fursunonin su ka shiga na nuna cewa akwai yiwuwar rikici ya barke daga bangaren falasdinawa idan har aka samu fursunan da ya mutu a gidan kaso.

Sauran 'yan Falasdinawa dai na kallon wadanda aka daure tamkar gwarzaye saboda suna ji da su sosai.

Karin bayani