Ana taro kan samun tsaftataccen ruwan sha

Image caption Kasashen Afirka na fama da rashin tsaftataccen ruwan sha

A ranar Litinin ne jami'an gwamnatocin kasashen Afirka da kwararru akan harkar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli za su fara taron makon ruwa na Afirka a birnin Alkahira na kasar Masar.

Taron, wanda za a kwashe kwanaki shida ana gudanarwa, zai tattauna akan kalubalen da kasashen ke fuskanta a fannin samar da tsaftaceccen ruwan sha da tsaftar muhalli ga al'ummomin kasashensu.

Mahalarta taron za su duba irin nasarorin da kasashen Afirka suka samu a kokarinsu na samar da tsaftataccen ruwa da inganta muhalli.

Kiyasi ya nuna cewa mutane kusan miliyan dari shida ne ba su da ingantaccen muhalli, yayin da mutane miliyan dari uku da talatin da biyar ba su da tsaftataccen ruwan sha a Afirka.

Haka kuma kiyasin ya nuna cewa fiye da yara dubu dari bakwai da hamsin ne ke mutuwa sanadiyar cutar amai da gudawa wadanda akasari rashin ingantaccen muhalli da tsaftataccen ruwan sha ke haddasawa a Afirka.

Karin bayani