An gwabza mummunan fada a kasar Syria

Ta'adin da aka yi a al Rastan na Syria
Image caption Ta'adin da aka yi a al Rastan na Syria

A kalla mutane talatin ne suka mutu cikin su har da sojoji 23 a wani kazamin fadan da ake gwabzawa a birnin Al-Rastan na Syria tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye.

Wata Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Syrian Observatory dake nan London ta ce 'yan tawayen sun yi kaca kaca da motoci masu sulke ukku a wajen birnin wanda 'yan tawayen ke iko da shi.

Sai dai kuma babu wata kafa mai zaman kanta data tabbatarda wannan ikirari.

Kasashen Turai na nuna fargaba akan cewa rikicin Syria zai iya yaduwa zuwa wasu kasahen, kamar Lebanon.

Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ya ce akwai bukatar Tarayyar Turai ta sa ido sosai a kan halin da ake ciki a kasar ta Syria.

Idan dai aka tabbatar da munin fada na baya-bayan nan da aka gwabza, hakan zai kasance wata alama ta kudirin gwamnatin Syria na sake kama garin na al Rastan, abun da zai iya yin illa ga shirin wanzar da zaman lafiya na Koffi Annan.

Karin bayani