Bikin auren zawarawa a Kano

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mata a Najeriya

A ranar Talata ne za a gudanar da gagarumin bikin auren zawarawa dari tare da angwayensu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Hukumar Hisbah ta Jihar, wacce ta dauki alhakin gudanar da bikin a madadin gwamnatin jihar, ta ce ta shirya tsaf don yin shagulgulan, wadanda sune na farko a tarihin jihar.

Auren na yau na daga cikin shirin aurar da zawarawa guda dubu da gwamnatin ta dauki aniyar yi.

Gabanin shagulgulan na yau, an yi wa zawarawan da mazajen da za su aura lacca Akan muhimmancin zaman aure; sannan an gudanar da gwajin cutar kanjamau don tabbatar da lafiyarsu.

Zawarawan da mazajensu sun shaidawa BBC cewa suna fatan auren da za a yi ya kasance mai danko.

Hukumar ta Hisbah ta ce ta bullo da shirin ne don rage mutuwar aure da sanya tarbiyyya a tsakanin al'ummar jihar.

Karin bayani