An rantsar da François Hollande a Faransa

François Hollande Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sabon Shugaban Kasar Faransa, François Hollande, yana duba faretin soja bayan rantsar da shi

Sabon shugaban kasar Faransa, François Hollande, ya yi kira da a samu wata sabuwar mafita ga Turai.

Yayin da ya ke jawabi bayan rantsar da shi, Mista Hollande ya ce zai gabatar da wata shawara a gaban Tarayyar Turai wacce za ta tallata bunkasar tattalin arziki, ba kawai rage yawan bashi ba.

An kaddamar da Mista Hollande ne a lokacin wani karamin biki a fadar Elysée, bayan an zabe shi saboda shirinsa na adawa da manufofin tsuke bakin aljihun da ake amfani da su a Tarayyar Turai.

Nan gaba a yau Talata kuma ana sa ran sabon Shugaban na Faransa zai gana da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, abin da ke nuni da muhimmancin rikicin da kudin bai-daya na euro ya fada ciki.

Dangantakar Faransa da jamus ce dai kashin bayan fikirar da Tarayyar Turai ta ginu a kanta a wannan zamanin.

A tarihance, babbar nasarar Tarayyar Turai ita ce kawar da yiwuwar gwabza yaki tsakanin Faransa da Jamus, kasashen da duhun rikice-rikicen da ke tsakaninsu ya lullube Nahiyar shekara da shekaru.

Sai dai kuma dangantakar ta sauya bayan wani lokaci: an yi shekaru da dama Faransa ce babba ta fuskar diflomasiyya yayinda Jamus ta mayar da hankali wajen gina tattalin arzikinta.

To amma yanzu karfin tattalin arzikin ne ya zama karfin fada-a-ji a Turai.

Saboda haka ne ma ba makawa Mista Hollande mai ra'ayin gurguzu zai je Jamus ne a matsayin karamin dan'uwa a dangantakar da ba tantama ta yi tsami.

Angela Merkel dai ba ta boye kwadayinta na ganin Nicolas Sarkozy mai ra'ayin mazan-jiya ya ci gaba da shugabancin Faransa ba.

Amma kuma yana da kyau a tuna cewa shi ma kanshi Mista Sarkozy sun dan samu rashin jituwa da Misis Merkel kafin su daidaita bayan wani lokaci.

Sai dai kuma matsalar tattalin arzikin da ta yiwa kasashen kudancin Turai kawanya ta sanya Shugabar Gwamnatin ta Jamus da sabon Shugaban na Faransa ba su da irin wannan lokacin. Amma fa dole ne su daidaita.

Don haka za a sa ido sosai a kan wannan ganawa tasu ta farko da nufin hango yadda dangantakarsu za ta kasance: Akwai damar yin cude-ni-in-cude-ka kuwa? Idan akwai, wanene zai cudi wa?

A takaice dai wannan al'amari zai dauki siffar fito-na-fito tsakanin tsuke bakin aljihu da bunkasar tattalin arziki.

A daya bangaren kuma, abin da ke a zahiri shi ne cewa, kamar yadda aka gani daga zabukan kananan hukumomin da aka gudanar kawanan nan a Jihar North Rhine Westphalia, Misis Merkel na fama da matsalolin siyasa a gida.

Shi ma kuma Mista Hollande, duk da burinsa na tallata bunkasar tattalin arziki, mutum ne da aka sani a matsayin mai matukar goyon bayan dunkulewar Turai.

Karin bayani