Hollande ya tattauna da Merkel akan Euro

hollande Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Francois Hollande na Faransa da Angela Merkel ta Jamus

Sa'o'i kadan bayan ya kama aiki sabon shugaban Faransa, Francois Hollande, ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a Berlin.

Sun tattauna akan matsalolin da suka dabai baye kasashe da ke amfani da kudin bai daya na Euro.

Shugaba Hollande ya kasance mai sukar shirin tsuke bakin aljuhun gwamnati, abunda ita kuma Angella Merkel ke goyi baya.

Mista Hollande dai ya dan yi lattin zuwa Berlin din saboda walkiya ta hana jirginsa sauka don haka sai da ya koma birnin Paris kana ya sake komawa Jamus din.

Tun farko ya nada Jean-Marc Ayrault, wanda tsohon amininsa ne a matsayin firayi minista sai dai kuma Jean-Marc Ayrault bai taba rige wani babban mukami ba.

Karin bayani